12 Yuli 2025 - 11:53
Source: ABNA24
Shugaban Lebanon Ya Ki Amincewa Da Kulla Alaka Da Isra'ila

Da yake watsi da duk wani daidaita dangantaka da gwamnatin Isra'ila, shugaban na Lebanon ya jaddada rashin goyon bayansa ga daidata alaka da gwamnatin da har yanzu take mamaye da wani yanki na kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahllul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: a martanin farko a hukumance kan kalaman ministan harkokin wajen kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata, ya ce Isra’ila na da sha’awar daidaita dangantakarta da Syria da Lebanon, Joseph Aoun ya jaddada cewa, batun daidaita al’amura ba ya cikin manufofin kasashen waje na kasar Lebanon a halin yanzu.

A cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar Labanon ta fitar, Aoun a ganawarsa da tawagar majalisar kula da huldar kasashen Larabawa da na kasa da kasa, ya banbanta tsakanin zaman lafiya da daidaita alakar, inda ya kara da cewa: Zaman lafiya shi ne a samu kasa da babu yaki, kuma yanayin yaki shi ne abin da ke damun mu a halin yanzu, amma batun daidaita alaka ba shi da wani matsayi a siyasar kasashen waje na Lebanon.

Ya yi kira ga sojojin Isra'ila da su janye daga yankuna biyar da har yanzu suke mamaye da su a kudancin Lebanon.

Bayan rikicin da ya shafe sama da shekara guda ana gwabzawa tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, wanda ya rikide zuwa fito na fito a watan Satumban da ya gabata, an kafa tsagaita wuta tsakanin Tel Aviv da Beirut a watan Nuwamba. To sai dai kuma duk da haka sojojin Isra'ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da kai hare-hare a yankuna daban-daban na kasar Labanon, musamman a kudancin kasar, inda sukan yi ikirarin kai hari kan 'yan kungiyar Hizbullah ko kuma wurarensu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha